Isa ga babban shafi
India

Ma’aikatan bankin Indiya na yajin aiki

Ma’aikatan kasar Indiya akalla miliyan daya ne su ka shiga wani yajin aikin kwana biyu, domin su nuna rashin jin dadinsu da wasu matakai da gwamnatin kasar ke so ta dauka wanda su ke ganin zai sa su rasa ayyukansu. 

Firaministan India, Manmohan Singh
Firaministan India, Manmohan Singh Getty Images/Shekhar Yadav
Talla

Kusan rassan bankuna akalla 87,000 basu bude ba inda kungiyar ma’aikatan bankin su ka yi ikrarin cewa kusan kashi 90 ne su ka shiga yajin aikin.

Babban sakataren kungiyar ma’aikatn bankin na kasar, Ashwani Rana ya tabbatar cewa sun a borin ne saboda matakan da ake so a dauka wadanda kan iya zama barazana ga ayyukansu.

Yan majalisun kasar ta Indiya na dab da saka hanu akan wasu dokoki da za su shafi bagaren na banki wanda za su bawa wasu kamfanoni damar mallakan mafi yawan bankunan.

Hannayen jari da darajar kudade sun fadi a kasar ta Indiya bayan shiga ma’aikatan yajin da za a kwashe kwanki biyu ana yin sa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.