Isa ga babban shafi
India

India ta yi nasarar mayar da wutar lantarkin kasar

Hukumomin kasar India, sun ce an yi nasarar mayar da wutar lantarki, bayan matsalar da aka samu, wadda ta jefa mutane sama da miliyan 600 cikin halin kunci.Shugaban kamfanin samar da wutar lantarkin, Chief SK Soone, ya ce an mayar da wutar a Arewacin kasar, tare da Gabashi da kuma Arewa maso Gabas, inda aka samu matsalar.  

Wata cibiyar samar da wutar lantarki a kasar India
Wata cibiyar samar da wutar lantarki a kasar India REUTERS/Adnan Abidi
Talla

Rahotanni sun ce, mutane sun shiga halin kakanikayi, saboda rashin sabo, inda wutar bada hannun dake hanyoyi suka tsaya cik, abinda ya haifar da rashin tsari wajen tuki, kana kuma wuraren cire kudi na ATM suka daina aiki.

Masu sana’oi ma sun koka kan matsalar, yayin da aka ruwaiti cewa, wasu daruruwan mahaka sun makale a karkashin kasa, saboda babu wutar da zata sanya inji ya hauro da su doran kasa.

Tsohon Ministan wutan lantarkin kasar Sulshilkumar Shinde, wanda aka mai karin girma zuwa Ministan cikin gida, ya ce ya kamata al’umar kasar India su gode wa injiniyoyin kasar domin irin kokarin da su ka yi.

Ya kara da cewa, a lokacin da wutan lantarkin kasar Amurka ta samu matsala sai da su ka dauki kwanaki hudu suna gyara, ya na mai cewa amma kasar India a cikin wasu sa’oi aka gyara wutar.

Sai dai gidajen jaridun kasar da na kasashen waje basu yi ma hukumomin kasar da dadi ba inda su ka nuna gazawar hukumomin wajen gyaran wutar.

Jaridar "Times of India" cewa ta yi a shafinta na farko, “Babu wuta babu mafita” a yayin da jaridar "Economic Times" ta rubuta cewa “babbar kasar India, Allah ya jikanki”.

Mutanen kasar da yawa su ka shiga cikin kunci a yayin da wutar ta dauke inda manyan masana’antu da kanana su ka yi ta kokawa.

“Na kashe rupees sama da 2,000 a jiya wajen siyan man da na zuba a cikin injin din wuta”, in ji Ram Prasad Kejriwal wanda ke da shagon sayar da kayayyaki.

Wata kungiyar masana’antu a kasar ta yi kiyasin cewa kudaden da aka yi asara dalilin daukewar wutar sun kai biliyoyin Rupees.

A shekarar da gabata, kasar India ta kara karfin yawan wutar tad a yawan megawatt 20,000.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.