Isa ga babban shafi
Syria

‘Yan tawayen Syria za su nemi taimakon al Qaeda idan aka juya masu baya

‘Yan tawayen Syria sun ce za su koma neman taimakon kungiyar al Qaeda idan babu wani goyon baya da suka samu daga kasashen Yammaci wajen yaki da gwamnatin shugaba Bashar al Assad.‘Yan tawayen Syria sun dade suna neman hadin kan kasashen Duniya domin daukar matakin kawo karshen zubar da jini a kasar.

Gungun 'Yan Tawayen Syria masu adawa da  Shugaba Bashar Assad
Gungun 'Yan Tawayen Syria masu adawa da Shugaba Bashar Assad REUTERS/Shaam News Network/Handout
Talla

“Ba mu bukatar Al Qaeda, amma idan babu wani goyon baya da muka samu, za mu kulla kawance da su,” inji Abu Ummar Kwamandan ‘Yan tawaye a gundumar Bab al Nasr yankin Aleppo.

A makon jiya ne ‘Yan tawayen suka nemi Majalisar Dinkin Duniya kafa dokar haramta shawagin jirage a Syria kamar yadda aka kafa dokar a Libya da ya taimakawa ‘Yan Tawaye samun galabar Kanal Gaddafi.

Abu Ummar yace yana da wahala su samu galabar Gwamantin Bashar Assad, domin yana da makamai masu guba da tankokin yaki da jiragen Yaki. Wannan ne yasa ‘Yan tawayen ke naman tallafi daga manyan kasashen Duniya.

Yawancin al’ummar kasar Syria mabiya Sunni ne amma an kashe shekaru kabilar Assad ta Alawite suna shugabancin kasar wadanda ke da alaka da mabiya Shi’a.

Bukatar ‘Yan tawayen yanzu ita ce, kasashen Larabawa da kasashen Yammaci su shiga tsakani domin kawo karshen yaki a Aleppo. Amma Mista Baraa yace idan hakan bai samu ba za su nemi taimakon al Qaeda.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.