Isa ga babban shafi
Afghanistan

Mutane da dama sun mutu a wani samame da Taliban suka kai a Kabul

Jami’an Tsaron Afghanistan sun ce Mutane Takwas sun Mutu a wani hari da Mayakan Taliban suka kai a wata Otel a birnin Kabul inda suka yi garkuwa da mata da yara kanana.

Jami'an tsaro a titunan birnin Kabul.
Jami'an tsaro a titunan birnin Kabul. REUTERS/Omar Sobhani
Talla

Jami’an tsaron sun ce an kai harin ne a wata Otel mai suna Spozhmai inda Attajiran Afghanistan ke sauka.

Kakakin ma’ikatar cikin gida Sadiq Saddiqi yace akwai Mata da Yara kanana da suka kububutar da Mayakan suka yi garkuwa da su.

Kakakin ‘Yan Sandan Afghanistan Hashmat Stanikzai, yace akwai fararen hula guda hudu da suka mutu da wasu masu gadin ginin Otel guda biyu da wani Dan Sanda.

Wannan harin na zuwa ne a dai dai lokacin da Dakarun kawancen NATO ke shirin ficewa daga Afghanistan.

A karshen shekarar 2014 ne Kungiyar NATO ta kudurta ficewa da Dakarunta 13,000 daga Afghanistan domin kawo karshen rikicin kasar wanda ya yi sanadiyar salwantar dinbim rayukan fararen hula.

A jiya alhamis ne Shugaba Hamid Karzai ya yi gargadin samun karuwar mutuwar Jami’an tsaro, yana mai cewa a kowace rana ana samun mutuwar Jami’an tsaro 20 zuwa 25.

Karzai ya amsa cewa Gwamnatinsa da kawayen shi na Turai sun gaza wajen aikin samar da tsaro a Afghanistan.

A baya baya nan akwai jerin hare hare da aka kai a Kandahar da birnin Khost da ke iyaka da Pakistan wadanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane sama da Ashirin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.