Isa ga babban shafi
MDD-Sahel-Gabas Ta Tsakiya

Kasashen Sahel da Gabas ta Tsakiya za su fuskanci barazanar karancin Abinci-MDD

Hukumar Kula da aikin noma da samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, ta yaba da hasashen samun yawaitar abincin a bana, amma tace wasu kasashen Yankin Gabas Ta Tsakiya da kasashen yankin Sahel suna fuskantar barazanar karancin abinci saboda rikici a yankunan.

Wani manomi a yankin kasar Chadi
Wani manomi a yankin kasar Chadi AFP PHOTO / OXFAM / IRINA FUHRMANN
Talla

Rahoton wanda kungiyoyin Noma da samar da Abinci suka fitar a bana, ya yi hasashen samun Karin sama da kashi uku na abincin da ake nomawa, saboda ci gaban da aka samu wajen noman Masara a Amurka.

Hukumar aikin noma da samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya tace an samu raguwar farashin abinci a watan Mayun bana, saboda fatar da ake da shi.

Rahotan yace, duk da wannan kyakkyawar fata, wasu sassan duniya da dama zasu fuskanci matsalar abinci, saboda rashin samun isasshen ruwan sama, da matsalar yanayi da kuma rikice rikice da ke janyo gudun hijira daga wata kasa zuwa wata kasa.

Shugaban Hukumar, Jose Graziano da Silva, yace tashin hankalin da ake samu a Yemen da Syria, zai shafi aikin gona.

Rahotan ya bayyana kasashe 35 na duniya, wadanda zasu bukaci taimakon abinci, kuma 28 daga cikinsu sun fito ne daga Afrika, wadanda suka hada da Jamhuriyyar Nijar da Mali da Chadi, sai kuma kasashen Yankin Gabas Ta Tsakiya da suka da hada da Afghanistan da Korea ta Arewa da Haiti, da kuma Iraqi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.