Isa ga babban shafi
China-Denmark

Ziyarar farko ta Hu Jintao a Denmark

A karon farko, shugaban kasar China, Hu Jintao, zai zama shugaban kasar na farko da zai kai ziyara zuwa kasar Denmark a ranar Alhamis kamar yadda Fira Ministan kasar ya fada.Shugaba Hu, zai jagoranci wata babbar tawaga da ta hada da ministocinsa da wasu manyan jami’an gwamnatin kasar.

Shugaban China Hu Jintao tare da Fira Ministan Rasha na yanzu Dmitry Medvedev
Shugaban China Hu Jintao tare da Fira Ministan Rasha na yanzu Dmitry Medvedev
Talla

Babban batun da ake hasashen zai mamaye ziyarar shi ne inganta huldar tattalin arzikin kasashen biyu.

Ana tunanin Shugaban Hu Jintao zai gana da shugaban kasar Denmark wanda shi ne shugaban kungiyar Tarayyar Turai a ziyarar shi ta kwanaki uku kafin ya wuce zuwa taron kasashe 20 masu karfin tattalin arzikin duniya da za a gudanar a kasar Mexico.

Kasashen biyu dai sun taba samun baraka a tsakaninsu a a shekarar 2009 a lokacin da tsohon Fira Ministan Denmark, Lars Loekke Rasmussen tare da Ministan harkokin wajen kasar su ka karbi ziyarar Shugaban yankin Tibet, Dalai Lama a wata ziyara da ya kai kasar Denmark.

A shekarar 2010, kasar Denmark ta nemi sasantawa da kasar China bayan ta aika da wata takardar diplomasiyya zuwa kasar China, domin nuna rashin goyon bayan yunkurin ballewar yankin Tibet daga kasar China.

A na kuma sa ran Hu Jintao zai gana da Saruniyar Denmark, Margereth ta biyu kafin ya gana da Fira Ministan kasar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.