Isa ga babban shafi
Iraqi

Harin Bom ya kashe mutane 57 a Iraqi da ke fama da rikicin siyasa

Wani harin bom a birnin Bagadaza ya yi sanadiyar mutuwar mutane 57 a dai dai lokacin da kasar ke fuskantar rikicin siyasa bayan bada sammacin kamo mataimakin shugaban kasa da ke zargin taimakawa ta’addanci. Harin wanda aka kai ya raunata mutane da dama, hari kuma na farko da ke nuna alamun barkewar rikici a cikin kasar.  

Hayakin da ke tashi a tsakiyar birnin Bagadaza bayan tashin bom a ranar Alhamis da ya kashe akalla mutane 10
Hayakin da ke tashi a tsakiyar birnin Bagadaza bayan tashin bom a ranar Alhamis da ya kashe akalla mutane 10 REUTERS/Mohammed Ameen
Talla

Wani Jami’in kiyon lafiya a birnin Bagadaza ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa AFP cewa an samu jerin hare hare guda takwas a tsakiyar kasar da arewa da kudu amma wani jami’in ma’aikatar harakokin cikin gida yace mutane 57 sun mutu, mutane 63 kuma suka samu rauni.

Jami’in kiyon lafiyar yace Harin Bom din ya shafi yankin Allawi, Bab al-Muatham da Karrada a tsakiyar birnin Bagadaza, da yankin Adhamiyah da Shuala da Shaab a yankin Arewaci da Jadriyah a gabaci da kuma al Amil a yankin kudancin kasar.

Wannan harin kuma na zuwa ne bayan da gwamnatin kasar ta bada sammacin cafko mataimakin shugaban kasa Tareq al-Hashemi, inda fira Ministan kasar Nuri al-Maliki ya bukaci Jami’an tsaron kasar mika shi ga hukuma.

Sai dai Hashemi ya musanta dukkanin zargin da ake mashi.

Tun samun wannan takaddamar ne mabiya Iraqiya suka kauracewa zauren Majalisa da taron Ministoci

Kasar Amurka ta yi kiran sasantawa tare da neman zaman lafiya a cikin kasar bayan ficewa da dakarunta inda Shugaban Amurka Barack Obama ya jaddada Iraqi zata zauna da kafafunta.

Tsakanni shekarar 2006 zuwa 2007 hare haren bama bamai sun yi sauki a Iraqi, kodayake an samu mutuwar mutane 187 a rikicin watan Nuwamba

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.