VATICAN-IRAN
Fadar Vatican na yunkurin hana kashe Ashtiani
FADAR Paparoma dake Vatican, tace tana yunkurin anfani da matakin diplomasiya, dan ganin kasar Iran bata aiwatar da hukuncin kisa kan Sakinah Ashtiani ba, matar nan da aka samu da laifin aikata zina.Kakakin fadar, Rev Federico Lombardi, yace fadar Vatican na adawa da hukuncin kisa a duniya baki daya.Kasar Brazil dake dasawa da Iran, tayi tayin baiwa Ashtiani matsayin Yar gudun hijira, amma Iran taki amincewa da haka.Tuni ake ta gudanar da zanga zanga a kasashen duniya da dama, dan ganin hukumomin kasar Iran, basu aiwatar da hukuncin kisan ba.
Wallafawa ranar: