Isa ga babban shafi
Philippines

An samu galabar tsohon Dan sanda wanda ya yi garkuwa da matafiya a Philippine

Bayan musayar wuta tsakanin ‘yan sanda da wani tsohon dan sanda Rolando Mendoza wanda ya yi garkuwa da wata mota mai dauke da fasinsoji, a yanzu haka dai ‘yan sandan sun ci karfin tsohon dan sandan kodayake an bayyana mutuwar mutane hudu a motar bayan da kuma dan sandan ya kashe kansa.Kwamandan ‘yan sandar Birnin Manila ya bayyana Rolando Mendoza da cewa an kore shi daga aiki ne saboda zargin fashi da makami, tirsasawa mutane dan karbar kudi da kuma mu’amala da masu fataucin miyagun kwayoyi.Mutane 22 aka bayyana a cikin motar da aka yi garkuwa da su inda aka fara sakin yara kanana shida hadi da wani dattijo daga cikin wadanda ke cikin motar.Bayan samun galabar al’amarin gomnatin Hong Kong ta sha alwashin daukar nauyin kai wadanda al’amarin ya shafa zuwa garuruwansu. 

Motar da aka yi garkuwa da ita a kasar philippines
Motar da aka yi garkuwa da ita a kasar philippines ©Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.