Isa ga babban shafi
Philippines

Hatsarin Mota Yayi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 41

A Kasar Philippines mutane 41 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani mummunar hatsarin mota a gabashin kasar.Daga ciki akwai ‘yan kasashen waje biyar.Da fari Rundunar ‘yan sandan kasar sunce mutane 49 ne suka mutu, wasu mutane tara kuma suka sami munanan raunuka.Jamiin ‘yan sandan yankin Baguio inda hatsarin ya auku, Reynaldo Telles yace cikin mamatan akwai dan kasar Indiya, da dan kasar Amirka.Karen motar wanda ya tsallake rijiya da baya, mai suna John Patrick Flores ya fadi cewa dreban motar yayi iyakacin kokari domin karo da wata itaciyar mangwaro dake kusa don gudun tsundumawa cikin kwazazzaban, amma kuma ya kasa.Karen -motar ya tsira da kananan raunuka. 

Masu aikin ceto wajen da akayi hatsarin na kasar Philippines
Masu aikin ceto wajen da akayi hatsarin na kasar Philippines rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.