Isa ga babban shafi

RSF ta yi tir da koran wani ɗan jaridar Faransa a ƙasar Togo

Ƙungiyar kare ƴan jaridu ta duniya RSF ta yi Allah wadai da matakin gwamnatin Togo na korar wani dan jarida Bafaranshe da ya yi ƙaurin suna wajen sukar lamirin gwamnati, kan fasalta ƙundin tsarin mulki.

Christophe Deloire, shugaban kungiyar kare 'yan jaridu ta kasa da kasa reporters sans frontières (RSF),3/5/23
Christophe Deloire, shugaban kungiyar kare 'yan jaridu ta kasa da kasa reporters sans frontières (RSF),3/5/23 © RFI
Talla

Cikin sanarwa da ta fitar ƙungiyar Reporteur Sans Frontire ta ce matakin hukumomin Togo sam bai da ce ba, na cin mutuncin dan jaridar kafin yi masa korar kare daga cikin ƙasar.

Thomas Dietrich

RSF ta ce ɗan jarida Thomas Dietrich da ke aiki da Ƙafar yada labaran yanar gizo ta Afrique 21, ya isa birnin Lome asabar din da ta gabata, inda jami’an tsaro suka tsare shi na tsawon sa’o’i 24 kafin gurfanar da shi gaban wata kotu da ta yanke masa hukuncin ɗaurin talala na watanni shida da kuma haramta masa shiga Togo tsawon shekaru biyar da kuma taran euro kusan 1000, kafin daga bisani aka titsa ƙeyarsa ta mota zuwa Benin.

Matakin na zuwa ne bayan wani sako da ɗan jaridar ya wallafa a shafinsa na X, inda ya alakanta shugaban kasar ta Togo Faure Gnassingbe da mai mulkin kama karya da ke neman dauwama a kan madufun mulki, bayan sauya ƙundin tsarin mulki.

Ƙasar Guinea ma ta kori Thomas

Wannan dai ba shine karon farko ba da aka taba koran ɗan jaridar daga wata kasar Afirka, domin kuwa ko a watan Janairun da ya gabata mahukuntan Guinea sun yi masa makamaiciyar wannan korar kan wani bincike da ya ke yi a kamfanin man fetir na kasar SONAP.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.