Isa ga babban shafi

Cibiyar Acre Impact Capital ta cike gibin kudaden yaki da sauyin yanayi a Afrika

Wasu tsoffin ma'aikatan bankin BNP Paribas biyu sun samar da kusan dala miliyan 100, a karkashin shirin samar da ababen more rayuwar da suka da ce da yanayin Afirka da ake bukatar biliyoyin daloli don aiwatarwa.

Wabi yanki da dumamar yanayi ta yiwa illa a Afrika.
Wabi yanki da dumamar yanayi ta yiwa illa a Afrika. REUTERS - Stephane Mahe
Talla

Cibiyar Acre Impact Capital, da ke da tsarin zuba jari a bangaren sauyin yanayi, na neman magance gibin da aka kiyasta ya kai dala biliyan 100 da matsalar sauyin yanayi ke samar wa duk shekara a nahiyar Afrika, musamman wajen samar da ayyukan more rayuwa ta hanyar samar da wani kaso na kudaden da ake bukata don gudanar da ayyukan.

Yawanci, hukumomin ba da lamuni na duniya ke bada kashi 85 na kudaden da ake bukata, sannan a samar da ragowar daga wasu bangarori na daban, sai dai kawo yanzu babu wani daga cikin bankunan da ke bada lamuni a bangaren da ya nuna aniyar samar da ragowar kudin, lamarin da ya sa aka samu sauyi a tsarin gudanar da ayyukan da aka shirya.

Shugaban cibiyar ta Acre Impact Capital Hussein Sefian ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa, har yanzu ba a cimma ko da rabin abinda ake bukata daga wajen bankunan ba, don haka suka shiga cikin lamarin don bada ragowar kashi 15 din da ake bukata.

Za dai a yi amfani da kudaden ne wajen gudanar da ayyukan da suka shafi makamashin da bashi da illa ga muhalli da kiwon lafiya da abinci da kuma ruwan sha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.