Isa ga babban shafi

Libya: Kungiyoyi biyu masu rike da makamai sun yi ba ta kashi

Rikici ya barke a tsakanin wasu karfafan kungiyoyi masu rike da makamai a Tripoli babban birnin Libya, a yayin da aka kwashe wajen sa'a guda ana fafatawa.

Dan ta da kayar baya a libya
Dan ta da kayar baya a libya ASSOCIATED PRESS - Hussein Malla
Talla

:An samu wata arangama tsakanin wasu karfafan kungiyoyi masu dauke da makamai na kasar Libya a babban birnin kasar Tripoli, lamarin da ya haifar da tashin hankali a tsakanin al'ummar kasar da ke shaukin murnar kammala azumin watan Ramadan, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka bayyana.

Rahotanni sun ce fadan da aka yi a daren ranar Alhamis zuwa Juma’a ya dauki kusan tsawon sa’a guda ana fafatawa, amma ba tare da an samu asarar rai ba.

Libya dai na ci gaba da fafutukar farfadowa daga shekaru da dama da aka shafe ana yaki da rudani bayan hambarar da gwamnatin marigayi Moamer Kadhafi a shekara ta 2011. Ko da yake an samu kwanciyar hankali a kasar mai arzikin man fetur a cikin shekaru hudu da suka gabata, sai dai ana samun tashe-tashen hankula akai-akai tsakanin kungiyoyin da ke dauke da makamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.