Isa ga babban shafi
AFIRKA

Tsadar rayuwa na kara ta'azzara yunwa a nahiyar Afirka - MDD

Majalisar dinkin duniya ta dora alhakin karuwar yunwa a nahiyar Africa da tsadar kayan abinci musamman a yammacin Afrika.

Wasu 'yan gudun hijira da ke dakon agajin jin kai a Djibo da ke Burkina Faso.
Wasu 'yan gudun hijira da ke dakon agajin jin kai a Djibo da ke Burkina Faso. AP - Sam Mednick
Talla

Akwai mutane akalla miliyan 55 da ke fama tsananin yunwa a Nahiyar Afrika, kuma hakan ne zai ci gaba da kasancewa cikin watanni masu zuwa.

Majalisar dinkin duniya ta sanya watannin Yuli da Agusta a matsayin wattannin da miliyoyin ‘yan Afrika zasu kasance cikin tashin hankali da fadi tashin ciyar da kansu a kowacce rana, tsananin da ya karu da ninki hudu idan an kwatanta da shekaru biyar da suka gabata.

Da suke bayani Ofishin hukumar samar da abinci na majalisar dinkin duniya da kuma asusun tallafawa kananan yara UNICEF sun ce kasashen da za’a fuskanci wannan matsala sun hadar da Najeriya, Ghana, Saliyo da kuma Mali, inda akalla mutane dubu 2,600 zasu fuskanci yunwa mai matukar tsakani kowacce rana a arewacin wadannan kasashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.