Isa ga babban shafi

Matsalar tsaro da ambaliya sun raba mutum miliyan 6 da matsugunansu- Gwamnatin Najeriya

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira da bakin haure ta Najeriya ta bayyana cewa sama da ‘yan kasar miliyan 6 da dubu 100 ne suka rasa muhallansu sakamakon matsalolin tsaro da iftila'i daban-daban.

Hoto don misali.
Hoto don misali. Médecins Sans Frontières
Talla

Babban Jami'in Hukumar Alhaji Tijjani Aliyu ne ya bayyana haka yayin wata ziyara da ya kai jihar Katsina, daya daga cikin jihohin kasar masu fama da matsakar tsaro.

A cewarsa, ya zuwa shekarar 2022, alkaluman hukumar sun nuna cewa mutane kusan miliyan 3 ne suka rasa matsugunansu, amma hadi da matsalar ambaliya da sauran iftila'in, an samu karin kashi 100 na irin wadannan mutanen da suka rabu da gidajensu.

Shugaban Hukumar ya bayyana cewa, "a halin yanzu gwamnati ba za ta iya samar wa kowa da matsuguni ba, saboda haka ne ta samar da shirye-shiryen horar da su sana'o'in hannu da za su taimak musu wurin dogara da kai".

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.