Isa ga babban shafi

Sakatare Janar na MDD ya koka kan rashin zaman Afirka mamba ta dindindin a Kwamitin Tsaro

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya koka kan rashin zaman Afirka mamba ta dindindin a Kwamitin Tsaro na majalisar.

Sakatare Jnar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Sakatare Jnar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. REUTERS/Lisi Niesner
Talla

Guterres ya caccaki Kwamitin Tsaro na Majalisar bisa rashin bai wa Afirka kujerar mamba ta dindindin a cikinsa.

‘Ta yaya za a amince da matakin hana bai wa Afirka mamba ta dindindin a Kwamitin Tsaro?’ in ji Antonio Guterres a sakon da ya wallafa a shafin X.

Ya kuma ci gaba da cewa "Dole ne kungiyoyi su yi nazari kan halin da duniya take ciki a yau, ba abin da ya faru shekaru 80 da suka wuce ba. Taron da za a yi a watan Satumba zai bayar da wata dama ta duba batun sauye-sauyen shugabancin duniya da sake kulla alaka bisa gaskiya, a cewarsa.

Guterres ya jaddada kiran da ya yi na kai kayan agaji da kuma tsagaita wuta a Gaza tare da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su.

"Ba zan yi kasa a gwiwa ba wurin yin kira a tsagaita wuta nan-take da kai kayan agaji da kuma sakin dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su ba tare da wasu sharudda ba," in ji shi.

Da yake tsokaci kan halin da ake ciki a Gaza wadda ke ci gaba da fuskantar hare-haren Isra'ila, ya ce: "Al'ummar Gaza suna mutuwa sakamakon harin bama-bamai da rashin abinci da kuma rashin hasken lantarki a asibitoci da kuma rashin magunguna."

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.