Faransa ta soke kudirin mika kanen tsohon shugaban Burkina Faso Blaise Compaire ga kotun kasar
Wallafawa ranar:
Faransa ta soke wani kudirin ministan shara’ar kasar na 2020, da ya bukaci tisa keyar François Compaoré, kanen tsohon shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaoré, a kasarsa, domin fuskantar shara’ar tuhumar aikata kisan shahararen dan jaridar nan Norbet Zongo, da wasu abukan tafiyarsa 3 a ranar 13 dsemba 1998.
kuduri da ya soke aniyar an tabbatar da shi ne tun ranar 13 ga watan desemba wannan shekara ta 2023, amma sai a ranar 20 ga watan na desemba ne, shugaban babban dakin shara’ar tisa keyar masu laifi, na babbar kotun birnin paris ya sanar a lokacin shara’ar, da ta bukaci soke kudurin tisa keyar ta François Compaoré, a Burkina Faso domin fuskantar shara’a da aka kudiri aniyar yi a 2017.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu