Isa ga babban shafi

Wani fitaccen mawakin Zambia ya kashe kansa kan zargin matarsa da cin amana

Wani mawaki dan kasar Zambia Nathan Mithi ya kashe kansa bayan da ya zargi matarsa Sabby Phiri da cin amanar aurensu.

Wani mawaki dan kasar Zambia Nathan Mithi ya kashe kansa bayan da ya zargi matarsa Sabby Phiri da cin amanar aurensu a ranar Alhamis, 14 ga Disamba, 2023.
Wani mawaki dan kasar Zambia Nathan Mithi ya kashe kansa bayan da ya zargi matarsa Sabby Phiri da cin amanar aurensu a ranar Alhamis, 14 ga Disamba, 2023. © Nathan Mithi facebook
Talla

An yi jana'izar Mithi, wanda aka bayyana a matsayin mamba na tawagar Ghetto Link, wata fitacciyar kungiyar mawaka a kasar a ranar Alhamis, 14 ga Disamba, 2023.

Sakon karshe

A cikin wani dogon bayanin kashe kansa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Mithi ya yi cikakken bayani kan abubuwan da suka faru a rayuwar aurensa da Phiri, inda ya zarge ta da cin amana da yaudara da rashin Imani da kuma neman salon rayuwa na katsaita.

“Idan kana karanta wanna sako, to tabbas na mutu”kamar yadda ya wallafa a shafin na sa.

Zargin lalata

Ya kuma bayar da labarin yadda ya kama matar tana lalata da wasu maza a kan gadon aurensu, ciki har da wani yaro dan uwan sa da kuma mai gidanda suka taba haya, wanda ya yi masa kacha-kacha cikin sakon.

“Me yasa na kashe kaina? Na yi haka ne domin ina sonta da gaske har cikin zuciyata. Zuciyata ta kasa daukar shirmen da ta tsunduma kanta ciki.”

“Amma a lokaci guda, ƙauna ce ta gaskiya gare ni. Na rasa begen soyayya, mace daya kawai nake gani a rayuwata ita ce.

Rashin tabbas kan abin da suka haifa

Mithi ya kara jaddada cewa ya bar Sabby da ’ya’ya biyar, “Uku nawa da biyu daga ubanni biyu daban-daban. Ban tabbata ko 'ya'yana ne ba.

Musanta zargin mijinta

Sai dai, a martanin da Phiri ta yi, ba ta amince da bayanin da mai dakin nata yayi ba kafin kashe kansa.

Gaskiyar labarina," tana mai cewa ta fuskanci cin zarafi a tsawon shekarun aurenta da marigayin.

Ta bayyana cewa mutuwar mijin nata ba ta da alaka da cin amana daga gareta, amma sai dai yawan bashin da ba za a iya shawo kansa ba, wanda ya taimaka masa matuka wajen rashin barci da kuma tashin hankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.