Isa ga babban shafi

Harin ta'addanci ya kashe mutum 31 a kasar Togo

Gwamnatin Togo ta sanar da mutuwar mutane 31 sakamakon ayyukan ‘yan ta’adda a cikin wannan shekara da muke bankwana da ita. 

Ana ganin jami'an tsaron kasar sun gaza wajen tunkarar matsalolin masu dauke da makamai.
Ana ganin jami'an tsaron kasar sun gaza wajen tunkarar matsalolin masu dauke da makamai. © REUTERS
Talla

Ta cikin wata sanarwa da ministar yada labaran kasar Yawa Kouigan ta fitar, ta ce wannan alkalma zasu baiwa kasar damar kara zage damtse wajen tabbatar da tsaro. 

Sanarwar da ministar ta fitar, ta ce ayyukan ‘yan ta’addar ya tafi da rayukan mutane 31, sai wasu 29 da suka jikkata da kuma uku da suka bata bat. 

Sanarwar ta kuma kara da cewa a bana kasar ta gamu da harin kwanton bauna 11 da tashin bama-bamai 9, sai wasu bama-bamai guda 20 da aka yi nasarar gano su kafin su tarwatse. 

Harin farko da aka samu a bana shine tashin Bam a yankin Kpendjal, dai-dai inda aka samu makamancin tashin bam a 2021, kuma yankin na gab da kan iyakar kasar da Burkina Faso. 

Arewacin kasashen Benin, Togo da kuma Ghana na fuskantar hare-haren ta’addanci nan da can, abinda ke jefa fargaba a zukatan ja’amar kasashen da ba’a saba samun labarin ta’addanci ba. 

Babu dai wani cikakken bayani game da irin matakan tsaro da kasar ke dauka don dakile yaduwar ta’addanci, amma dai a mabanbantan lokutan shugaban kasar Faure Gnasingbe na shan alawashin hana ta’addanci tasiri a kasar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.