Isa ga babban shafi

Sama da yara miliyan 1.6 za su fuskanci bala'in yunwa a Sudan ta Kudu

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, sama da kananan yara miliyan 1 da dubu 600 ‘yan kasa da shekaru biyar za su gamu da matsalar rashin abinci mai gina jiki nan da shekara mai zuwa a Sudan ta Kudu sakamakon karuwar cututtukan da suka samo asali daga ambaliyar ruwa.

Wasu kananan yara dauke da tukunya da roba a Sudan ta Kudu
Wasu kananan yara dauke da tukunya da roba a Sudan ta Kudu AFP - TONY KARUMBA
Talla

Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce za a samu wannan matsalar ce saboda karuwar cututtukan da ake samu daga ruwan sha mara tsafta bayan fama da ibtila’in ambaliyar a kasar ta Sudan ta Kudu.

Tun lokacin da wannan jinjirar kasar ta samu ‘yanci a shekarar 2011, ta yi ta fama da matsaloli kala-kala da suka hada da tashe-tashen hankulan da suka lakume rayuka da jerin ibtila’o’i masu aukuwa da kansu da tabarbarewar tattalin arziki har ma da rikita-rkitar siyasa.

A baya-bayan nan dai, mutanen Sudan ta Kudu musamman wadanda ke rayuwa a yankunan da ruwa ya mamaye, na ta fafutukar neman hanyar samun abinci  a daidai lokacin da cututtuka ke yaduwa.

Ambaliyar ruwa ta shanye yankuna masu fadi a lardin Rubkona, lamarin da ya tilasta wa mazauna yankin baki daya komawa can wani karamin tsibiri don ci gaba da rayuwa tun a shekarar 2021, yayin da tsadar kayayyakin abinci ta haura da fiye da kashi 120 tun daga watan Afrilun da ya gabata.

Yanzu haka an yi hasashen cewa, wannan lardi na Rubkona da ke yankin arewacin Sudan ta Kudu zai gamu da gagarumar musibar yunwa nan da watan Afrilun shekara mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.