Isa ga babban shafi

Tashin hankali ya raba mutane kusan miliyan 7 da gidajensu a Congo - IOM

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya IOM, ta ce rikice-rikicen da ke karuwa sun tilasta wa mutane miliyan 6 da dubu 900 rabuwa da gidajensu a Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo, galibinsu a gabashin kasar.

Motar sulken dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a sansanin 'yan gudun hijira na Rhoe da ke lardin Ituri, da ke arewa maso gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo.
Motar sulken dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a sansanin 'yan gudun hijira na Rhoe da ke lardin Ituri, da ke arewa maso gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo. REUTERS - PAUL LORGERIE
Talla

Cikin rahoton da wallafa hukumar IOM ta ce shekarun da aka shafe sassan Jamhuriyar ta Congo musamman gabashin kasar na fama da hare-haren kungiyoyi masu dauke da makamai, da masifun ambaliya, ko zaftarewar  kasa ko da kuma aman wuta daga tsaunuka, sun taka rawa wajen tsananta halin tagayyarar da mutane suka yi a kasar.

Bayanan da Majalisar Dinkin Duniya ta tattara sun nuna cewar yankunan da suka fi sama da matsalar ‘yan gudun hijirar sun hada da lardin Arewacin Kivu, da Kudancin Kivu, da Ituri da kuma Tanganyika.

A arewacin Kivu kadai, mutane kusan miliyan daya ne suka rasa matsugunansu sakamakon rikicin da ake fama da shi tsakanin kungiyar 'yan tawayen M23 da sojojin Jamhuriyar Congo.

IOM ta ce domin saukakawa miliyoyin mutanen radadin da suke ciki, tun cikin watan Yunin wannan shekara ta 2023 ta gina matsugunan wucin guda 3,347 tare da raba kayayyakin bukata akalla dubu 7,715 wadanda basu kunshi abinci ba. Sai dai ta yi gargadin cewa a halin yanzu tana fuskantar karancin kudaden gudanar da ayyukan tallafin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.