Isa ga babban shafi

Alamu na nuna cewa za a je zagaye na biyu a zaben shugaban kasar Liberia

Sakamakon farko da hukumar zaben kasar Liberia ta fitar a yau Talata ya cewa za a je zagaye na biyu a zaben shugaban kasar tsakanin shugaba George Weah da abokin hamayyarsa Joseph Boakai, sabida yadda suke tafiya kankankan.

Alamu na nuna cewa za a je zagaye na biyu a zaben shugaban kasar Liberia.
Alamu na nuna cewa za a je zagaye na biyu a zaben shugaban kasar Liberia. REUTERS - CARIELLE DOE
Talla

Kashi 94 na sakamakon zaben da hukumar ta fitar, ya nuna cewar Boakai ya samu kashi 43 da digo 70, yayin da Weah da ke neman wa’adi na biyu ya samu kashi 43 da digo 65.

‘Yan takara biyun nan ne ke kan gaba, kan sauran abokan takararsu 18 a zaben da aka gudanar a ranar 10 ga watan Oktoban nan.

Hukumar ta ce kawo yanzu an kammala kirga kusan kashi 93 na kuri’u a rumfunan zabe, wanda ya nuna cewar Weah ko Boakai babu wanda ya samu rinjayen da ake bukata ya lashe zabe a zagayen farko.

Makonni biyu bayan sanar da sakamakon zaben ne dai ya kamata a gudanar da zaben zagaye na biyu, in har ba a shigar da wasu korafe-korafe ba.

Wannann ne dai karo na farko da aka gudanar da zabe a kasar ta Liberia tun bayan ficewar sojojin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 2018, bayan kawo karshen yakin basan kasar da yayi sanadiyar mutuwar mutane sama da dubu dari biyu da 50.

Tuni dai kungiyar kasashen yammacin Afrika ECOWAS da kuma kungiyar kasashen Afrika AU su ka taya gwamnatin kasar murnar gudanar da zabe cikin lumana, tare da samun mutane da dama da suka fito suka yi zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.