Isa ga babban shafi

Gwamnatin arewacin Libya ta dage lokacin da ta sanya na fara gyaran birnin Darna

Mahukuntan Libya sun dage lokacin da aka sanya na fara gyaran birnin Darna da ambaliyar ruwan watan jiya ta dai-daita.

Irin barnar da ambaliyar ruwa ta yiwa birnin Darna
Irin barnar da ambaliyar ruwa ta yiwa birnin Darna © Jamal Alkomaty / AP
Talla

Ta cikin wata sanarwa da gwamnatin arewacin kasar ta fitar, ta ce dage fara gyaran ya zama wajibi la’akari da yadda har yanzu kwamitin da aka sanya don duba taswirar birnin da kuma irin ginin da ya dace ayi suka gaza mika sakamakon binciken su.

Bayanai sun tabbatar da cewa kwamitin ya tsayar da ranakun Laraba da Alhamis na makon gobe a matsayin ranar da zasu mikawa gwamnati da kuma yi mata fashin baki kan rahoton nasu.

A cewar Sabr Al-Jabani shugaban kwamitin, irin barnar da ambaliyar ruwan tayi ne dalilin da ya haddasawa aikin binciken nasu tafiyar wahainiya kasancewar wasu guraren basa iya shiguwa har yanzu.

A baya dai an tsayar da ranar 10 ga watan Octoban da muke ciki a matsayin ranar da za’a fara kafa harsashin gyaran birnin Darna.

Kafin fara kafa dambar dai za’a gudanar da wani taro da gwamnatin arewacin kasar ta gayyaci kasashen duniya da hukumomi.

Har yanzu dai ba’a sanya wata rana da za’a gudanar da taron ko kuma fara kafa harsahsin aikin gyaran ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.