Isa ga babban shafi

Gwamnatin Congo ta karyata zargin hambarar da shugaba Denis Nguesso

Gwaamnatin Congo Brazaville ta musanta zargin yi wa shugaban kasar Denis Sassou Nguesso juyin Mulki, bayan da ya kwashe tsawon shekaru 39 ya na shugabantar kasar.

Gwamnatin Congo Brazaville ta karyata zargin yiwa shugaba Denis Sassou Nguesso juyin mulki.
Gwamnatin Congo Brazaville ta karyata zargin yiwa shugaba Denis Sassou Nguesso juyin mulki. © AP - Francois Mori
Talla

A ranar Lahadi ne aka fara yada batun juyin mulkin na Congo a kakafen sada zumunta, sai dai ministan yada labarai na kasar Thierry Moungalla ya karyata zargin, inda ya ce shugaba Nguesso ma baya kasar ya na birnin New York na Amurka don halartar taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78.

 

Haka nan shafin yada labarai na gwamnatin kasar, ya fidda sanarwar da ke karyata zargin juyin mulkin da aka ce an yi wa shugaban mai shekaru 79 a duniya.

 

Shugaba Denis Nguesso, ya hau kujerar shugabancin kasar da ke tsakiyar Afirka mai arzikin man fetur, ta hanyar juyin mulki a shekara ta 1979.

 

Shugaban Congo-Brazzaville, Denis Sassou-Nguesso.
Shugaban Congo-Brazzaville, Denis Sassou-Nguesso. AFP - EDUARDO SOTERAS

A watannin baya-bayan nan an fustanci juyin mulki a nahiyar Afrika, na karshe shine wanda sojoji su ka yi a Gabon da ke makwaftaka da kasar ta Congo a watan Agustan da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.