Isa ga babban shafi

'Yan Nijar na jin jiki saboda wutar da Najeriya ta katse musu

'Yan kasuwa musamman masu kananan sana'o'i a Jamhuriyar Nijar sun bayyana irin wahalar da suke sha a yanzu bayan da Najeriya ta katse wutar lantarki da take bai wa kasar, a wani bangare na takunkuman karayar tattalin arziki da Kungiyar ECOWAS ta kakaba wa kasar.

Turakun wutar lantarki a China
Turakun wutar lantarki a China AP - Andy Wong
Talla

An dai katse wutar ce saboda juyin mulkin da sojoji suka yi wa shugaba Mohamed Bazoum, yayin da 'yan kasuwar ke cewa, suna fuskantar babban kalubale a harkokinsu na kasuwanci, inda ala tilas suka koma amfani da janareto wanda ba ya biya musu bukatarsu.

Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken rahoton Salissou Issa daga Maradi

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.