Isa ga babban shafi

Mutane da dama sun mutu a kasar Kamaru sakamakon rugujewar wani bene

Akalla mutane 12 ne suka mutu yayin da 21 suka jikkata, wannan Lahadin a kasar Kamaru, sakamakon ruftawar wani gini a cibiyar cinikayyar kasar Douala.

Akalla mutane 12 ne suka mutu yayin da 21 suka jikkata, wannan Lahadin a kasar Kamaru, sakamakon ruftawar wani gini a cibiyar cinikayyar kasar Douala.
Akalla mutane 12 ne suka mutu yayin da 21 suka jikkata, wannan Lahadin a kasar Kamaru, sakamakon ruftawar wani gini a cibiyar cinikayyar kasar Douala. © Actu Camaroun
Talla

Ma’aikatan kashe gobara da hukumomin yankin suka ce wani bene mai hawa hudu ya ruguje kan wani ginin da misalin karfe daya na dare a arewacin birnin Douala.

Charles Elie Zang Zang, wani kancila a karamar hukumar Douala, ya kara da cewa jami'an ceto na neman wadanda suka tsira karkashin baraguzan ginin.

Asibitin Laquintinie na Douala ya bayyana cewa an kwantar da mutane 13, inda wata yarinya 'yar shekaru uku da wata budurwa 'yar shekara 19 -- suka mutu.

Wasu yara uku daga cikin wadanda suka jikkata na karbar kulawar gaggawa a sashin kula da kananan yara.

Kasar Kamaru ta yi kaurin suna a samun rugujewar gine-gine masamman a birnin Douala, a shekarar 2016 kiminin mutane biyar sun mutu a irin wannan yanayi a Douala da hukumomi suka zargi rashin inganci da bin ka’idar gine-gine  ke haifar da lamarin.

A cikin watan Yunin wannan shekarar, hukumomin yankin sun gano gine-gine 500 da ke cikin hadarin rugujewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.