Isa ga babban shafi

Aikin hadin gwiwa tsakanin sojojin Faransa da Nijar ya kashe 'yan ta'adda a iyakar Mali

Sojojin Faransa da Jamhuriyar Nijar sun kaddamar da wasu hare haren hadin gwuiwa a iyakar Mali da Burkina Faso abinda ya basu damar hallaka tarin shugabannin ‘Yan ta’adda da kuma kama guda biyu daga cikin su. 

Jirgin Chinook kenan, lokacin da yake mika makamai ga dakarun aikin hadin gwiwa da sojojin Faransa a Mali da Nijar.
Jirgin Chinook kenan, lokacin da yake mika makamai ga dakarun aikin hadin gwiwa da sojojin Faransa a Mali da Nijar. État-major des armées
Talla

 

Wannan samamen hadin gwuiwar tsakanin sojojin Faransa da na Jamhuriyar Nijar ya haifar da mahawara sosai a Birnin Yammai dake Nijar, dangane da nasarar da suka samu wajen murkushe manyan ‘yan ta’addan da suka addabi yankin. 

Masu tofa albarkacin bakinsu akan nasarar na bayyana kashe ‘yan ta’addan a matsayin tasirin hadin kan da sojojin kasashen biyu ke yi wajen aiki tare. 

Rahotanni sun ce an samu nasarar hallaka wadannan ‘yan ta’addan ne a yankin Gorouol dake kusa da iyakokin Mali da Burkina Faso. 

Bayanai sun ce, yayin kaddamar da hare haren sojojin sun yi nasarar kama biyu daga cikin fitattun ‘yan ta’addan da ake nema ruwa a jallo a yankin Bankilare, bayan an sanya kudi akan kowanne guda daga cikin su. 

Mutanen sun hada da Abou Maryam da akewa lakabi da Zaid wanda aka kama ranar alhamis 6 ga watan Yuli a kauyen Ingra dake arewacin Gorouol, kuma aka bayyana shi a matsayin mai kaddamarwa a kungiyar yan ta’addan. 

Shi kuwa mutum na biyu da aka kama, an bayyana shi a matsayin Sita Ousseini, wanda ake yiwa lakabi da Loukoumane. 

An dai kama shi ne a tsakanin kauyen Lamdou da Amarsingue kusa da birnin Tera, kuma shima yana da cikin jagororin ‘yan ta’addan a yammacin Tera. 

Majiyar soji tace yana daga cikin wadanda suka jagoranci harin da aka kai Seytenga daga gabashin Burkina Faso, Wanda ya hallaka fararen hula sama da 100. 

Rahotanni sun ce dakarun kasashen biyu sun kuma yi nasarar kwace tarin makamai sakamakon hare haren. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.