Isa ga babban shafi

Faransa ta musanta jita-jitar kame sojojinta a kan iyakar Chadi da Sudan

Faransa ta musanta zargin kame wasu dakarun Sojinta da Chadi ta yi akan iyakar kasar da Sudan bayan da suka shiga yankin ba bisa ka’ida, lamarin da ma’aikatar tsaron Faransar ke cewa sabanin fahimta ne aka samu tsakanin bangarorin biyu.

Wasu Sojojin Faransa da ke yaki da ayyukan ta'addanci a Sahel.
Wasu Sojojin Faransa da ke yaki da ayyukan ta'addanci a Sahel. AFP - MICHELE CATTANI
Talla

Wasu faya-fayan bidiyo da suka bazu a kafofin sada zumunta na zamani sun nuna yadda wasu sojojin Chadi ke tisa keyar wasu sojoji sanye da kakin Faransa wadanda ke rarrafawa yayinda sojojin na Chadi ke bin bayansu rike da bindigogi wani guda kuma ke amsa waya a gefe guda lamarin da ke nuna cewa suna karbar umarni ne kan tisa keyar sojojin.

Karkashin faifan bidiyon dai, daidaikum mutane sun rika tofa albarkacin bakinsu, inda wasu ke bayyana sojojin na Faransa a matsayin masu aikin satar ma’adinai a bangare guda kuma wasu ke bayyana su da masu liken asiri.

Mahukuntan Chadi sun rika ganin kiraye-kirayen bukatar kamewa tare da tuhumar sojojin na Faransa tun bayan fitar bidiyon na ranar 8 ga watan nan.

Sai dai ma’aikatar tsaron Faransa ta yi karin haske game da bidiyon wanda ta bayyana da sabanin fahimta daga bangarorin biyu ta na mai cewa hadakar Sojin na Faransa da Chadi na aikin bayar da tsaro ne a yankin Abeche na gabashin Chadi mai tazarar kilomita 48 da inda Sojojin Chadin suka tsaresu lokacin da suke fito rangadin tituna lura da yadda damuna ke kara karfi.

A cewar ma’aikatar tsaron ta Faransa, Sojin da ke aiki a shingen binciken basu da masaniya game da aikin hadakar Sojin na Faransa a Abeche kuma tuni suka saki sojojin tare da basu damar ci gaba da aikinsu bayan fahimtar juna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.