Isa ga babban shafi

Kasashe fiye da 40 a sassan duniya na bikin karrama yara 'yan Afirka

Yau 16 ga watan Yuni ake bikin ranar girmama yara ‘yan Afirka, inda za a gudanar da taruka kan zagayowar ranar a ciki da wajen nahiyar.

Wasu yara 'yan Jamhuriyar Congo yayin cin abinci a wani sansanin 'yan gudun hijira na wucin gadi, bayan tserewa daga muhallansu, sakamakon kazamin fada tsakanin sojojin gwamnati da gungun 'yan ta'adda. 10 ga Nuwamba, 2021.
Wasu yara 'yan Jamhuriyar Congo yayin cin abinci a wani sansanin 'yan gudun hijira na wucin gadi, bayan tserewa daga muhallansu, sakamakon kazamin fada tsakanin sojojin gwamnati da gungun 'yan ta'adda. 10 ga Nuwamba, 2021. REUTERS - ABUBAKER LUBOWA
Talla

Babban makasudin ware wannan rana a kowace shekara shi ne domin karrama daliban da aka yi wa kisan kiyashi a garin Soweto na Afirka ta Kudu cikin shekarar 1976, yayin da suke zanga-zangar adawa da rashin daidaito wajen bayar da ilimi a karkashin mulkin wariyar launin fata na ‘Apartheid’.

A shekarar 1991 kungiyar Tarayyar Afirka ta ayyana 16 ga watan na Yuni a matsayin Ranar Yara na Afirka, wadda a duk shekara ake tsara taruka akan kare ‘yancin yara, musamman a nahiyar.

Wasu 'yara 'yan gudun hijira bayan karbar tallafin litattafai da sauran kayayyakin karatu a makarantar Sarema da ke yankin Mopti a kasar Mali.
Wasu 'yara 'yan gudun hijira bayan karbar tallafin litattafai da sauran kayayyakin karatu a makarantar Sarema da ke yankin Mopti a kasar Mali. © UNHCR/Alassane Guindo

Taken bikin ranar ta yau shi ne ‘yancin samun damarmarki’. ‘A kula da yara tare da sauraron bukatunsu’

Taruka fiye da 100 ne ake sa ran za su gudana a kasashe sama da 40, domin bikin ranar ta karrama yaran na Afirka.

Bikin na bana ya zo ne bayan da wata kididdiga ta bayyana cewar, nahiyar ke dauke da yara miliyan 30 daga cikin miliyan 57 a fadin duniya wadanda ba sa iya zuwa makaranta.

Baya ga kalubalen rashin samun ilimin kuma akwai batu na lafiya, inda duk da cewar an samu raguwar mutuwar yara ‘yan kasa da shekaru 5 da kashi 45 cikin 100 a tsakanin 1990 zuwa 2012, bincike ya nuna cewar har yanzu ana samun akalla yaro guda cikin rukunan yara 6 a Afirka, wadanda ba sa kai wa shekaru 5 a raye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.