Isa ga babban shafi

Yara miliyan 20 da basa zuwa makaranta ka iya zama ‘yan Boko Haram- Obasanjo

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi gargadin cewa wajibi ne gwamnatin kasar ta dauki matakan gaggawa wajen magance matsalar tarin kananan yaran da ake da su wadanda basa zuwa makaranta ko kuma a fuskani karuwar mayakan Boko Haram miliyan 20.

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo REUTERS/Joe Penney
Talla

A jawabinsa gaban taron kasa kan sauya fasalin tsarin ilimi mai zurfi da majalisar wakilan kasar ta shirya, Obasanjo ya ce matukar ba a dauki matakan da suka dace wajen mayar da yara miliyan 20 makaranta ba ko shakka babu akwai hadarin su iya tsunduma cikin kungiyar Boko Haram.

Taron wanda ya gudana a Abuja ya mayar da hankali kan kalubalen da yajin aikin kungiyar malaman jami’o’I ta Najeriyar ASUU ke haifarwa ga rayuwa ko kuma makomar daliban kasar.   

Tsohon shugaban na Najeriya, Olusegun Obasanjo ya ce wajibi ne gwamnati ta bullo da wasu shirye-shirye da za su rage yawan yaran da basa zuwa makaranta don dakile barazanar yiwuwar fadawarsu mugayen hannu.

Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa yaran da basa zuwa makaranta babu ta hanyar da za su iya taimakawa wajen gina kasa, dalilin da ke nuna bukatar da ake da ita wajen tilastawa yara karatu don ci gaban kasar.

A cewar Obasanjo akwai bukatar tilasta zuwa makarantun Firamare da Sakandire ga dukkanin yaran Najeriya, yana mai cewa gwamnati ta gaza wajen iya rage yawan yaran da basa zuwa makaranta musamman a arewacin kasar da ake fama da matsalar ta’addanci.

Cikin yara miliyan 244 da basa zuwa makaranta a sassan Duniya, Najeriya ke da adadin yara miliyan 20 da ke matsayin kashi 10 na jumullar yaran marasa zuwa makaranta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.