Isa ga babban shafi

An kawo karshen cutar Marburg a kasar Tanzania - WHO

Mahukuntan Tanzania sun sanar da kawo karshen annobar cutar Marburg, bayan da hukumar lafiya ta duniya ta sanar da barkewar ta watanni biyu da suka gabata. 

Kamar cutar Ebola, tzazzabin Marburg na haifar da aman jini, gudawa da zazzabi mai tsanani.
Kamar cutar Ebola, tzazzabin Marburg na haifar da aman jini, gudawa da zazzabi mai tsanani. AFP/File
Talla

Tun bayan sanar da barkewar cutar ta kama mutane 8, cikin su kuma guda 6 sun mutu a cutar da ke farawa daga tsananin zazzabi, da ta faro daga yankin Kagera da ke arewa maso yammacin kasar. 

A cewar WHO, wannan shine karo na farko da aka sami barkewar cutar, a kasar mai yawan mutane miliyan 62. 

Mutum na karshe da gwaji ya tabbatar baya dauke da kwayar cutar a Tanzania, an gudanar da gwajin ne a ranar 19 ga watan Afrilu, wanda ya kawo karshen wa'adin kwanaki 42 da WHO ta baiwa kasar, na tabbatar da cewa ta kawo karshen cutar.

Bisa bayanan hukumomin lafiya, cutar ta soma yaduwa ne daga dabbobi irin su Jemage, zuwa ga dan adam.

Har yanzu dai babu wani rigakafi, ko kuma wanda zai magance kwayar cutar kai tsaye da aka samar daga hukumomin lafiya, sai dai ana ci gaba da bincike a kai, in ji WHO.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.