Isa ga babban shafi

'Yan jarida sun yi zanga-zangar neman 'yancin jarida a kasar Tunisia

'Yan jarida da dama a kasar Tunisiya sun gudanar da zanga-zanga a wajen sashen bincike na 'yan sanda na El Gorjani da ke Tunis domin nuna goyon bayansu ga wasu 'yan jarida biyu da ake bincike a kansu.

'Yan jarida na zargin gwamnati da haramta 'yancin fadin albarkaccin baki.
'Yan jarida na zargin gwamnati da haramta 'yancin fadin albarkaccin baki. REUTERS - ZOUBEIR SOUISSI
Talla

Masu zanga-zangar ciki har da daya daga cikin 'yan jaridar da aka gayyata Elyes Gharbi, sun yi tir da abin da suka kira yunkurin tauye 'yancin 'yan jarida a kasar.

Kiraye-kirayen ‘yan jaridar biyu ya biyo bayan amfani da dokokin yaki da ta’addanci da aka yi wajen yanke hukuncin shekaru biyar a gidan yari da aka yankewa Khalima Guesmi, bayan daukaka kara kan hukuncin daurin shekara daya da aka yanke masa a watan Nuwamba.

An samu Guesmi da laifin kwarmata wasu bayanai da gangan da suka shafi kutse, sa ido kan sauti ko tattara bayanai, a cewar lauyan da ke kare shi.

Mahdi Jlassi, shugaban kungiyar 'yan jarida ya ce akwai manufa ta siyasa wajen shirya bita da kulli ga ‘yan jaridar da ake tuhuma.

A ranar Litinin ne aka tsare wasu dalibai biyu ‘yan kasar Tunisia bayan da suka wallafa wata waka a shafukan sada zumunta da ke sukar ‘yan sanda da dokokin hana shan muggan kwayoyi.

Jlassi ya kara da cewa a halin yanzu an gurfanar da 'yan jarida kusan 20 gaban kuliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.