Isa ga babban shafi

Masu yawon bude ido da aka sace a kan iyakar Nijar da Burkina Faso sun kubuta

An gano wasu masu yawon bude ido ‘yan kasar Maroco guda  biyu da aka sace tun cikin watan Afrilun da ya gabata  a wani guri dake kan iyakar Burkina Faso da Jamhuriyar Nijer, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar ta Maroco MAP ya sanar.

Taswirar dake nuna sassan Jamhuriyar Nijar da wasu kasashe makwafta.
Taswirar dake nuna sassan Jamhuriyar Nijar da wasu kasashe makwafta. © USAID/FFP
Talla

Bayan da suka baro Maroko a ranar 19 ga watan janairun da ya gabata, Abderrahmane Serhani, malamin makarantar sakandare da ya yi ritaya yana dan shekaru 65 da Driss Fatihi, dan kasuwa mai shekaru 37 a duniya, dukkaninsu masu sha’awar tukin keke nE, manufarsu ita ce ziyartar birnin ziyartar kasa mai tsarki domin gudanar da aikin Hajji.

 

Sun ratsa kasar Mauritaniya ne kafin zuwa  Burkina Faso daga nan kuma su tsallaka cikin jamhuriyar Nijer, da zumar isa mashigin kasar Saudiya a cewar kungiyar masu yawon buda ido kan kekuna ta Souss-Massa, da wadannan matuka keke biyu suka kasance mambobi a cikinta ta.

 

Amma a karshen watan Maris, bayan isarsu kasar Burkina Faso ba a sake jin duriyaru ba daga shafinsu na Facebook da suke bada labarin halin da suke ciki a wannan mawuyaciyar tafiya mai nisa da suka tarka.

 

Yanzu haka matukan kekunan biyu na jiran a maidasu garinsu na asali kuma har yanzu babuwani ko wata kungiya da ta dau nauyin garkuwa da mutanen biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.