Isa ga babban shafi

Ambaliya ta raba sama da mutane dubu 200 da muhallansu a Somalia

Kimanin mutane dubu  200 ne suka rabu da muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa, bayan da kogin Shabelle ya zarce gabarsa har ya mamaye tituna da gidaje.

Sama da mutane dubu 200 ne ambaliya ta daidaita a Somalia.
Sama da mutane dubu 200 ne ambaliya ta daidaita a Somalia. © AFP/Hassan Elmi
Talla

Ala tilas mazauna garin Beledweyne a yankin Hiran na kasar suka bar gidajensu, inda aka gansu dauke da kayayyakinsu a kansu,  suna tafiya a  kan titunan da ambaliyar ta mamaye.

Mataimakin gwamnan yankin, Hassan Ibrahim Abdulle  ya ce mutane 3 sun mutu sakamakon wannan ambaliyar.

Masana sun ce ana samun  karuwar yayanyi mai tsanani irin wannan ne sakamakon sauyin yanayi da ake fuskanta, kuma nahiyar Afrika, wadda kasonta na ayuyukan da ke haddasa sauyin yanayi shine mafi kankanta, ta fi fama da tasirinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.