Isa ga babban shafi

Kasar Chadi ta kori Jan Christian Gordon Kricke jakadan Jamus

Hukumomin Djamena sun  baiwa jakadan Jamus da ke kasar sa'o'i 48 na ya fice daga kasar saboda "rashin mutunta ayyukan diflomasiyya" a cewar hukumomin wannan  kasa a ranar Juma'a.“Gwamnatin ta bukaci mai girma Jan Christian Gordon Kricke, jakada mai cikakken iko na Tarayyar Jamus, da ya bar  Chadi cikin sa’o’i 48,” in ji mai magana da yawun gwamnatin Aziz Mahamat Saleh, a wata sanarwa da ya fitar.

Shugaban gwamnatin sojin Chadi kenan, Idris Deby
Shugaban gwamnatin sojin Chadi kenan, Idris Deby © theguardian
Talla

Hukumomi Chadi ba su bayar da cikakken bayani kan tuhumar da ake yi masa ba. Majiya a ofishin jakadancin Jamus a Djamena ta shaida wa AFP bisa sharadin boye sunanta cewa "ba a tuntube su a hukumance ba,", wanda ta ce ta karanta sanarwar da aka fitar a shafukan sada zumunta.

Taswirarar kasar Chadi
Taswirarar kasar Chadi © RFI

Jakadan Jamus mai suna Jan Christian Gordon Kricke ya taba zama jakada a kasar Chadi tun watan Yulin 2021, inda ya yi irin wannan aiki a kasashen Nijar, Angola da Philippines. Ya kuma kasance wakilin Jamus na musamman a yankin Sahel.

Wata majiyar gwamnati ta shaida wa AFP bisa sharadin sakaya sunanta cewa mahukuntan kasar sun soki jami'in diflomasiyyar musamman da "shishigi da yawa" a cikin siyasar kasar ta Chadi, da kuma kokarin raba kan 'yan kasar Chadi".

Da aka tambaye ta, tawagar ta Jamus ba ta mayar da martani cikin gaggawa ba.

Janar Mahamat Idriss Deby Itno ya hau karagar mulki kasar Chadi a watan Afrilun 2021, bayan mutuwar mahaifinsa, Idriss Deby Itno, da aka kashe a fagen yaki da 'yan tawaye bayan ya jagoranci wannan babbar kasa ta Sahel tsawon shekaru 30. Mahamat Deby ya kuma yi wa Chadi da kasashen duniya alkawarin mayar da mulki ga farar hula ta hanyar "zabe a karkashin tsarin dimokuradiyya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.