Isa ga babban shafi

Chadi ta saki 'yan tawaye 380 da aka yi wa afuwa bayan zarginsu da kashe Deby

Gwamnatin Chadi ta ce ta saki ‘yan tawayen kasar 380, bayan da ta yi musu afuwar hukuncin daurin rai da rai da aka yanke musu a bara. 

Shugaban gwamnatin sojin Chadi kenan, Idris Deby
Shugaban gwamnatin sojin Chadi kenan, Idris Deby © theguardian
Talla

 

Tun farko an kama mutanen ne bisa zargin su da hannu a kisan tsohon shugaban kasar Idris Deby Itno . 

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ruwaito cewa wakilin sa ya ga mutane sama da 30, sanye da baki da farin kaya bayan sun cire kayan gidan yarin, yayin da suka hau layi ana kuma raba musu shaidar sallamar su da aka yi. 

Bukin sakin fursunonin

A wajen bikin sakin ‘yan tawayen da aka haska a gidan talabijin din kasar ya nuna yadda aka saki ‘yan tawayen su 350 a gaban ministan shari’a Mahamat Ahmat Alhabo. 

Rahotanni sun bayyana cewa an yankewa mutanen su 400 hukuncin daurin rai da rai a ranar 21 ga watan Maris din bara, sai dai kuma a yanzu an yafe musu. 

Dukannin mutanen dai mambobin kungiyar tawayen mafi girma ta kasar wato FACT ne, kuma an kama su ne tun farkon shekarar 2021.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.