Kamala Harris ta isa Ghana a ziyarar kasashen Afrika 3 da ta faro
Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris ta isa birnin Accra na kasar Ghana a yammacin yau lahadi, zangon farko a ziyarar da za ta gudanar cikin kasashe uku na nahiyar Afirka.
Wallafawa ranar:
Baya ga kasar ta Ghana, Harris za ta ziyarci Tanzania da kuma Zambia, inda a kasar Ghana, za ta tattauna da shugaba Nana Akufo-Addo da kuma shugabannin wasu kungiyoyin fararen hula na kasar.
Yayin da a Ghana Harris ke shirin karfafa gwiwar kungiyoyin fararen hula tare da shawarwari ga gwamnatin kasar game da halin matsin tattalin arzikin da kasar ke fama da su, can a Tanzania kuwa mataimakiyar shugaban na Amurka za ta tabo batun 'yanci da kuma baiwa mata damarmakin shiga a dama da su a lamurran kasar.
Wannan ziyara dai na zuwa ne a dai dai lokacin da Amurka ke kokarin janyo kasashen Afrika cikinta bayan da Rasha ke kokarin zabe musu uwar gijiya sakamakon yadda ta ke karfafa ikonta ta fuskar karfin soji a nahiyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu