Isa ga babban shafi

An kama fiye da tan uku na tabar wiwi a gabar tekun Morocco

Sojojin ruwan kasar Morocco suka kama fiye da tan uku na tabar wiwi a gabar tekun Nador, wani gari mai iyaka da yankin Melilla na kasar Spain a arewa maso gabashin kasar, in ji wata majiyar soji a yau asabar.

Gonar wiwi
Gonar wiwi Getty Images/EyeEm - Amine Bettach / EyeEm
Talla

Jami’na tsaron kasar ta Morocco sun kama wasu jiragen ruwa masu tafiya da sauri guda biyu dauke da jakunkuna 85 da ke da nauyin fiye da ton uku", in ji majiyar MAP. kamfanin dillancin labarai kasar.

Birnin Nador na daya daga cikin yankuna masu tsaunuka na Rif, wanda shine babban yankin da ake noman tabar wiwi a Morocco.

Ganyen wiwi
Ganyen wiwi AP - Charlie Riedel

Masarautar ita ce mafi girma a Duniya da ke samar da itacen tabar wiwi a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

'Yan sandan Morocco sun kwace kusan tan 100 a cikin shekara ta 2022, raguwar rabin idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, a cewar rahoton shekara-shekara na Babban Daraktan tsaron kasar ta Morocco (DGSN).

Morocco ta yanke shawarar a cikin 2021 don halatta "amfani da doka na likitanci, kayan kwalliya da itacen wiwi ga masana'antu.

Za a fara aiki da sarrafa tabar wiwi don masana'antu a watan Nuwamba shekarar 2024 a arewa maso gabashin masarautar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.