Isa ga babban shafi

Tanzaniya ta amince bututun man Uganda ya ratsa kasarta

Gwamnatin Tanzaniya ta amince a gina bututun danyen mai na dalar Amurka biliyan 3 da milyan 500, duk da adawa da hakan da masu fafutukar kare hakkin bil'adama da muhalli suka yi game da babban aikin.

Taswirar bututn mai karkashin shirin EACOP
Taswirar bututn mai karkashin shirin EACOP © wikipedia
Talla

Bututun mai tsawon kilomita 1,443 kwatankwacin mil 900, zai yi jigilar danyen mai ne daga manyan rijiyoyin mai da ake hakowa a tafkin Albert da ke arewa maso yammacin Uganda zuwa tashar ruwa ta Tanzaniya da ke gabar tekun Indiya domin isar da shi zuwa kasuwannin duniya.

Ana sa ran kasar Uganda za ta fara hako nata danyen man a shekarar 2025, kusan shekaru ashirin kenan da aka gano man a kasar.

Aikin bututun ya bukaci sahalewar kasashen biyu, kuma a watan Janairu ne Uganda ta ba da lasisi ga kamfanin da zai gudanar da aikin, bututun danyen man a gabashin Afirka.

Kamfanonin kasashen Faransa China, tare da kamfanonin mai na kasashen Uganda da Tanzaniya ne suka shirya wannan aikin na dala biliyan 10.

Wannan gagarumin aiki ne, zai kasance mai alfanun gaske ta fuskar tattalin arziki ga kasashen Gabashin Afrika, inda da yawa ke rayuwa cikin talauci.

Sai dai ya fuskanci suka mai karfi daga masu fafutukar kare hakkin bil adama da muhalli wadanda suka ce hakan na barazana ga yanayin yankin da kuma rayuwar dubun dubatar mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.