Isa ga babban shafi

Matsalar tsaro da karancin abinci za ta mamaye tattaunawar taron AU a Adis Ababa

Yau juma’a aka bude babban taron kungiyar kasashen Afrika na shekara-shekara a birnin Addis Ababa na Habasha, taron da ake sa ran tattauna batutuwa masu alaka da karancin abinci, fari, matsalolin tsaro da kuma fadadar ayyukan ta’addanci a yankin Sahel ya mamaye shi. 

Taron AU na bana zai mayar da hankalli a kan matsalar karancin abinci da tsaro.
Taron AU na bana zai mayar da hankalli a kan matsalar karancin abinci da tsaro. AP
Talla

 

Taron na kwanaki 3 da ya faro daga yau, 17 zuwa 19 ga wata na samu halartar shugabannin kasashen nahiyar 55 baya ga sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterress da kuma Charles Michel na Tarayyar Turai. 

Taron na AU na zuwa ne  a dai dai lokacin da matsalolin tsaro ke ci gaba da fadada a kasashen yammacin Afrika, a bangare guda tsananin yunwa da fari ke barazana a kasashen yankin kuryar gabashin Afrika, dai dai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke cewa ambaliyar ruwa ta raba mutane miliyan 44 a bara.   

Yayin bude taron a safiyar yau juma’a, jami’an diflomasiyyar AU sun gabatar da jawabi na musamman kan halin da ake ciki a gabashin jamhuriyyar demokradiyyar Congo mai fama da yaki baya ga matsalolin tsaron da ake gani a kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Guinea baya ga Sudan wadanda dukkaninsu suka fuskanci juyin mulki a 2021 da 2022. 

Shugabannin za kuma su yi magana da murya guda don neman kujerar din-din-din ga nahiyar a zauren Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyar kasashen G20. 

Haka zalika yayin taron shugabannin za kuma su tattauna don tabbatar da yarjejeniyar kasuwancin bai daya, da bisa ka’ida ya kamata a faro tun shekarar 2021. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.