Isa ga babban shafi
Tarayyar Afrika

An yi taron sake fasalta dokokin Tarayyar Afrika

Shugabannin kasashen Afirka uku ne suka halarci wani taron share fage kan yadda za a yi wa dokokin kungiyar Tarayyar Afirka garambawul a birnin Conakry na Guinea.

Shugaban Guinea Alpha Condé da Paul kagame na Rwanda a Conakry
Shugaban Guinea Alpha Condé da Paul kagame na Rwanda a Conakry CELLOU BINANI / AFP
Talla

An yi taron ne karkashin jagorancin shugaban Guinea Alpha Conde kuma shugaban Tarayyar Afrika na yanzu da kuma shugaba Idris Deby na Chadi da Paul Kagame na Rwanda.

Babbar manufar taron dai ita ce samar da sabbin shawarwari kan yadda za a yi wa wasu daga cikin dokokin tafiyar da kungiyar ta Afirka garambawul domin su dace da tafiyar zamani da kuma manyan kalubalen da ke gaban nahiyar.

Shugaban Hukumar Kungiyar ta Tarayyar Afrika Moussa Mahamat Faki ya ce taron Koli na kungiyar da za a yi cikin watan Yuli mai zuwa a birnin Kigali na Rwanda, zai mayar da hankali ne kan wannan batu na fasaltar dokokin tafiyar da kungiyar.

Taron da shugabannin uku ya jaddada matsayin taron shugannin kungiyar da aka gudanar watanni biyu da suka gabata, na ganin cewa kungiyar ta samar wa kanta kudaden tafiyarwa domin ci gaba da dogara da kanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.