Isa ga babban shafi

Cancer na kashe mutane dubu 700 duk shekara a Afrika- WHO

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce akalla mutane miliyan 1 da 100 ne ke kamuwa da cutar Cancer ko kuma sankara duk shekara a Afirka, daga cikin adadin kuma cutar na kashe kimanin mutane dubu 700 a nahiyar duk shekara.

Ana dai ci gaba da samun karuwar masu fam ada cutar ta Cancer a sassan Afrika.
Ana dai ci gaba da samun karuwar masu fam ada cutar ta Cancer a sassan Afrika. Getty Images - fstop123
Talla

Babbar darakar hukumar ta WHO mai kula da Afirka, Dr Matshidiso Moeti ce ta bayyana alkaluman a ranar lahadi, yayin jawabin da ta gabatar, kan ranar wayar da kai kan cutar Cancer ta duniya, da aka yi wa taken “inganta dabarun yaki da cutar Kansa da kuma hada gwiwa domin yakarta” 

Daraktar ta kara da cewar, bincike kwararru ya yi hasashen cewa nan da shekarar 2050, nahiyar Afirka za ta kasance dauke da kusan kashi 50 cikin 100 na yawan yara kanana masu dauke da cutar Cancer a duniya. 

Kididdigar ta kuma yi hasashen za a rika samun kashi 56.3 cikin 100 na yara masu ciwon dajin a tsakanin mutane miliyan guda a Afirka. 

Hukumar lafiya ta duniya ta yi gargadin cewa, muddin ba a dauki matakan da suka dace wajen dakile cutar ba, to fa nan da shekarar 2030, za a iya afkawa cikin hatsarin rasa rayukan mutane miliyan 1 duk shekara a maimakon mutane dubu 700. 

WHO ta ce yanzu haka kasashe 12 ne a Afirka ke da cikakken shiri da tsarin yaki da cutar Cancer zalika ta na kan talllafawa wasu karin kasashen 11 domin cimma wannan cigaba. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.