Isa ga babban shafi

Sudan ta kudu ku ajiye ''kiyayya''- Fafaroma Francis

Fafaroma Francis ya yi kira a yau Lahadi ga al'ummar Sudan ta Kudu da su ajiye ''makamin kiyayya'' a wajen wani taron baje koli a ranar karshe ta ziyarar aikin da ya kai kasar da ke fama da tashe-tashen hankula da fatara.

Fafaroma Francis lokacin da yake bankwana da jama'a
Fafaroma Francis lokacin da yake bankwana da jama'a AP - Jerome Delay
Talla

Daruruwan masu ibada ne suka yi ta tururuwa zuwa mujami'ar John Garang da ke Juba babban birnin kasar domin ganin Fafaroma Francis wanda ya mayar da zaman lafiya da sulhu a taken ziyararsa ta kwanaki uku a Sudan ta kudu.

"Mu ajiye makaman kiyayya da ramuwar gayya,mu kawar da kyama da suka zama ruwan dare tare da haddasa kabilanci tsakanin mu," in ji Fafaroma Francis a cikin jawabin sa a birnin Juba.

Ya bayyana fatan cewa al'ummar Sudan ta Kudu, kasar da ta shafe kusan rabin rayuwarta tana fama da yaki, za ta gina makoma mai sulhu.

Jama'a sun daga tutocin kasar tare da rera wakar zaman lafiya yayin da Fafaroma na Argentina ya zagaya cikin taron jama'a a cikin motarsa.

 Da kamala wannan ziyara Fafaroma Francis ya tashi daga Juba zuwa Roma. Ana sa ran zai gudanar da taron manema labarai a cikin jirginsa tare da Archbishop na Canterbury da kuma mai gudanar da babban taron Cocin Scotland, wadanda suka raka shi a wannan tafiya.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.