Isa ga babban shafi

Amurka ta lafta wa gungun 'yan IS dake Afrika ta Kudu takunkumai

Amurka ta sanar da lafta takunkumai kan gungun mayakan IS da ke kasar Afrika ta Kudu da kuma kamfanonin da ke karkashin kulawarsu, matakin da ke matsayin ramuwar gayya kan goyon bayan da suke bai wa kungiyar ta ‘yan ta’adda.

Shugaban Amurka, Joe Biden.
Shugaban Amurka, Joe Biden. AP - Alex Brandon
Talla

Baitul Malin Amurka ya ce, makasudin daukar wannan matakin shi ne dakile duk wani goyon baya da kungiyar ke samu tare da hana fadada ayyukanta a yankin  Afrika.

Babban jami’i a Baitil Malin Amurka, Brian E. Nelson ya ce, suna sanya ido kan wasu tsirarun mutane da ke da alaka da ISIS a Afrika ta Kudu da kadororin da suka mallaka, wadanda kuma suka taka gagarumar rawa wajen dabbaka ayyukan ta’addanci da miyagun laifuka a yankin.

Amurka ta sanya sunayen mutane hudu da wasu kamfanoni takwas a cikin wani bakin kundi, inda ta daskarar da duk wata kadara da suka mallaka a Amurka tare da hana su cin moriyar duk wani tsarin sarrafa kudade.

Mista Nelson ya kara da cewa, Amurka za ta ci gaba da hadin guiwa da Afrika ta Kudu domin hana ISIS duk wata dama ta fakewa da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki wajen tura kudade ga mambobinta.

Mutanen da takunkumin ya shafa sun hada da Nufael Akbar da Yunus Mohamed Akbar da Mohamed Akbar da Umar Akbar wadanda aka ce dukkaninsu ‘yan uwan juna ne na jini.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.