Isa ga babban shafi

Masu rajin kare muhalli na zanga-zanga kan sauyin yanayi a jamhuriyar Congo

Masu rajin kare muhalli sun gudanar da zanga zanga a Kinshasa babban birnin Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo, kwanaki kalilan gabanin fara taron sauyin yanayi a birnin cikin watan gobe.

Zanga-zangar bukatar yaki da dumamar yanayi.
Zanga-zangar bukatar yaki da dumamar yanayi. REUTERS/Mike Hutchings
Talla

Ana saran Kinshasa ya karbi taron share fagen COP27 da zai gudana a watan Nuwamba a kasar Masar, inda masu ruwa da tsaki daga sassan daban daban na Afirka zasu halarci taron domin gabatar da matsayin su.

Sai dai taron zai gudana ne a daidai lokacin da Congo ta sanar da shirin sayar da rijiyoyin mai 27, sabanin gargadin da masu kare muhalli keyi akai.

Jiya juma’a, a kalla mutane sama da 200 suka shiga zanga zangar da aka fara, inda suke bayyana adawar su da amfani da man fetur.

Congo na daya daga cikin kasashen dake da arzikin ma’adinai daban daban cikin su harda man fetur da sinadarin lithium da ake yin batir da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.