Isa ga babban shafi

Ghana ta yi nasarar murkushe cutar Marburg a kasar

Ghana ta yi ikirarin kawo karshen cutar Marburg wadda ta bulla a kasar kimanin watanni biyu da suka gabata sannan ta kashe ikalla mutane biyu a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya.

An gano kwayar cutar Marburg karo na biyu a Ghana da ke Yammacin Afirka
An gano kwayar cutar Marburg karo na biyu a Ghana da ke Yammacin Afirka © CDC/ Dr. Frederick Murphy
Talla

Hukumar Lafiya WHO, ta tabbatar da samun cikakkun bayanai daga ma’aikatar lafiya ta kasar Ghana da ke tabbatar da kawo karshen cutar bayan kwanani 42 ana sa-ido a kan wadanda suka harbu da ita ko kuma wadanda suka yi cudanya da su.

An gano cutar ce a ranar 7 ga watan Yulin da ya gabata a Ghana, to sai dai tuni aka samu bullarta a wasu kasashe na nahiyar da suka hada Angola, Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, Guinea, Afirka ta Kudu da kuma Uganda.

Daraktar Hukumar Lafiya WHO a yammacin Afirka Dr Matshidiso Moeti, ta ce Marburg kwayar cuta ce mai tayar da hankali, tare da jinjina wa Ghana dangane da namjin kokarin da kasar ta yi domin shawo kanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.