Isa ga babban shafi
Zaben Kenya

Zaben Kenya: 'Yan kasa sun yi addu'ar zaman lafiya saboda fargaba

Al'ummar Kenya sun yi addu'ar samun zaman lafiya a jiya Lahadi, yayin da suke dakon sakamakon karshe na zaben shugaban kasar, wanda 'yan takara biyu da suka hada da mataimakin shugaban kasa William Ruto da Raila Odinga ke tafiya kan-kan-kan, kamar yadda sakamakon zaben da ya fara fita ya nuna.

Wasu daga cikin jami'an Hukumar Zaben Kenya da ke cikin tsaka mai wuya wajen tattara sakamakon zaben shugabancin kasar da aka gudanar.
Wasu daga cikin jami'an Hukumar Zaben Kenya da ke cikin tsaka mai wuya wajen tattara sakamakon zaben shugabancin kasar da aka gudanar. REUTERS - MONICAH MWANGI
Talla

Tun da safiyar jiya Lahadi ne dai ta bayyana mataimakin shugaban kasar William Ruto ke kan gaba da tazara kadan akan abokin hamayyarsa Raila Odinga a kuri’un da ake kidayawa kai-tsaye daga hukumar zabe mai zaman kanta a Kenyan, kafin daga bisani a katse nuna kidayar kuri'un, matakin da har yanzu hukumar zaben ba ta bayyana dalilin daukarsa ba, bayan kirga.

A halin da ake ciki, an kidaya sama da kashi 70 cikin 100 na kuri’un da aka kada a zaben kasar ta Kenya, yayin da wasu alkaluma da jaridar Daily Nation da ke kasar ta wallafa suka nuna cewar, William Ruto ya samu kashi 52.5 na kuri'un da aka kada, yayin da Odinga ya samu kashi 46.7.

Bayanai sun ce, cikin dare aka girke ‘yan sandan kwantar da tarzoma a ciki da wajen harabar hukumar zaben Kenya da ke Nairobi babban birnin kasar, bayan da hatsaniya ta tashi a tsakanin wakilan jam’iyyu a daidai lokacin da ake kidayar kuri’un da aka kada, inda suka rika tuhumar juna da yunkurin yin magudi.

Kungiyoyi fiye da 12 da suka hada da na farar hula da na kwadago da kuma kungiyoyin kare hakkin bil adama na Amnesty International da kuma Transparency International a kasar ta Kenya ne suka fitar da wata sanarwa a jiya Lahadi inda suka bukaci a kwantar da hankula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.