Isa ga babban shafi
Zaben Kenya

'Yan siyasa ne ke hana mu fitar da sakamako - Hukumar Zaben Kenya

Hukumar Zaben Kenya ta ce, tana samun jinkirin tattara sakamakon zaben shugabancin kasar, inda ta dora laifi kan jam’iyyun siyasa, yayin da kuma kafafen yada labaran kasar suka daina sanar da sakamakon wucen-gadi.

Shugaban Hukumar Zaben Kenya rike da abin magana, Wafula Chebukati.
Shugaban Hukumar Zaben Kenya rike da abin magana, Wafula Chebukati. REUTERS/Baz Ratner
Talla

An dai gudanar da zaben shugabancin kasar a ranar Talatar da ta gabata cikin lumana, ba kamar sauran zabukan da aka yi a shekarun baya ba, inda aka samu tashe-tashen hankulan da suka yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Ganin jinkirin fitar da sakamakon ne a wannan karo, ya sanya jama’ar kasar ta Kenya fargabar abin da ka iya biyo baya, a daidai lokacin da sakamakon wucen-gadi ke nuni da cewa, William Ruto da Raila Odinga na tafiya ne kan-kan-kan wajen samun yawan kuri’un da aka kada.

Yanzu haka dai, hankula sun karkarta ne kan Hukumar Zaben Kasar wadda ake sa ran ta fitar da sakamako cikin hanzari, kuma duk tsawon jinkirin da za a samu, to lallai ba zai taba wuce ranar 16 ga wannan wata na Agusta ba.

Yau dai kwanaki hudu  kenan da hukumar zaben ke tattara sakamako, yayin da shugaban hukumar, Wafula Chebukati ya zargi wakilan jam’iyyun siyasar kasar da haddasa jinkirin ta hanyar yi wa jami’an hukumar tijara da kuma addabar su da tambayoyi marasa ma’ana a cewarsa.

Chekabuti dai ya roki jam’iyyun siyasar da su yi hakuri su daina katse ayyukan jami’an hukumar zaben, yana mai cewa, ci gaba da hakan zai sa su gaza fitar da sakamakon cikin lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.