Isa ga babban shafi

An cika Shekaru 10 da kisan fararen hula a Marikana ba tare da hukunci ba

An cika shekaru 10 da kisan gillar da ‘yan sanda suka yiwa fararen hula a gab da katafariyar mahakar Marikana ta Afrika ta kudu, sai dai har zuwa yanzu iyalai da ‘yan uwan wadanda abin ya shafa na ci gaba da jiran adalci daga mahukuntan kasar.

Zanga-zangar Marikana da ta kai ga kisan tarin mutane.
Zanga-zangar Marikana da ta kai ga kisan tarin mutane. MUJAHID SAFODIEN / AFP
Talla

Tun farko ma’aikatan kamfanin Platinum na 3 mafi girma a Duniya wato Lonmin Company da ke gab da babbar mahakar Marikana a kasar ta Afrika ta kudu ne suka faro zaman darshan don bukatar karin albashi zuwa Rand dubu 12 a kowanne wata.

Daga zaman darshan din tirjiya don neman karin albashin ne yajin aikin ya juye zuwa tarzoma tsakanin jami’an ‘yan sanda da ma’aikatan da suka tsaya a harabar kamfanin wanda ya kai ga harbe-harbe.

Nolufefe Noki wanda ya zamo fuskar zanga-zangar ma’aikatan sakamakon jagorantar gangamin da kuma kasancewa baki a gare su, yafe da wani koren bargo ya umarci dandazon ma’aikatan su dunkule hannu tare da dagawa, har zuwa kashe shi a ranar 16 ga watan na Agustan 2012.

Yayin harbin da jami’an ‘yan sandan suka y ikan ma’aikatan, bayanai sun ce sun kashe mutane 34 nan ta ke yayinda suka jikkata wasu 78 wanda ke matsayin kisa mafi tayar da hankali da Afrika ta kudu ta gani tun bayan kawo karshen mulkin danniya a shekarar 1994.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.