Isa ga babban shafi

'Yan Kenya sun kagu a fitar da sakamakon zabe

Al’ummar Kenya na dakon sakamakon zaben shugabancin kasar da aka gudanar cikin lumana, yayin da alkaluman wucen-gadi ke nuni da cewa, ana tafiya ne kan-kan-kan tsakanin manyan ‘yan takara guda biyu wato William Ruto da kuma Raila Odinga.

Jami'an Hukumar Zaben Kenya sun shafe tsawon dare suna kidayar kuri'u.
Jami'an Hukumar Zaben Kenya sun shafe tsawon dare suna kidayar kuri'u. REUTERS - BAZ RATNER
Talla

Mataimakin shugaban kasa, William Ruto da kuma magudun ‘yan tawayen kasar da yanzu haka ke samun goyon bayan jam’iyya mai mulki, Raila Odinga, dukkaninsu sun yi alkawarin rungumar kaddara, amma duk da haka ‘yan kasar ta Kenya sun gaza mancewa da tashe-tashen hankulan da suka a gani a zabukan shekarun baya da suka gabata.

Jami’an Hukumar Zaben Kasar ta IEBC da ke shan matsin lamba, sun shafe tsawon dare suna ta kidayar kuri’u karkashin kulawar masu sanya ido, kuma duk irin jinkirin da za a samu na fitar da sakamakon zaben, babu shakka ba zai wuce ranar 16 ga wannan wata na Agusta ba.

Shugaban Hukumar Zaben, Wafula Chebukati ya roki ‘yan Kenya da su ci gaba da hakuri duk da cewa, sun kagu su ga an fitar da sakamakon zaben cikin gaggawa domin kauce wa zarge-zargen tafka magudi kamar yadda aka gani a zabukan baya.

A jiya Talata ne jama’ar Kenya da suka yi dogayen layuka tun da asuba, suka kada kuri’unsu a zabuka shida da suka hada da na shugaban kasa, gwamnoni, sanatoci, ‘yan majalisa da na wakilan mata har ma da na kananan hukumomi.

Koda yake a wannan karo,  an samu karancin fitowar masu kada kuri’a, idan aka kwatanta da zabukan da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.